WASIYOYIN DA ALLAH (S.W.T) YA SANAR DA MANZON ALLAH (S.A.W) DON YA SANAR DA MUTANE
Wasiyoyin ANNABI (s.a.w)
1→ Kada mutum yayi shirka da Allaah a cikin bauta, ko cikin ayyukansa, ko sunayansa, saboda Allaah yana gafarta dukkan zunubai banda shirka
2→ Kyautatawa iyaye, don Allaah a waje da dama ya gwama bautarsa da kuma kyautatawa iyaye, saboda haka duk wanda yayi xaya ya bar xayan, to bai yiwa Allaah biyayya ba
3→ Kada mutum ya kashe 'ya'yansa don talauchi, daya sameshi bayan haihuwa, saboda haka Allaay yace mune zamu azurtaku da su 'ya'yan da muka baku, a wani waje a alqur'aani yace kada ku kashe 'ya'yanku don tsoron talauchi, wato tsoron da kuke idan kun haihu talauchi bazai barku kuyi musu tarbiyya ba, mune zamu azurtasu da kuma ku
4→ Kada kuma mutum ya kusanchi Alfasha, wato ko zina ko makamantanta, a voye, ko a sarari, domin ita alfasha, wani wahala ne ka mutum a nan duniya, kuma shiga wuta in mutum bai tuba ba ranar gobe qiyama
5→ Kada mutum ya kashe wata rai haka kawai indai ba da hakkin Allaah ba, kamar mai aure da yayi zina, ko wanda yayi kisan kai, kom kuma wanda yayi Ridda, ko kuma wanda aka kama yana fashi da makami da sauransu
6→ Kada mutum yaci dukiyar maraya sai dai ta yanda shari'a ta yarda, a wani waje Allaah ya nuna duk mai cin dukiyar maraya baiyi imaani da ranar tashin alqiyamah ba
7→ Kuma mutum ya cika ma'auni da kuma sikeli, wato in mutum zaiyi awo ya cika mudu, haka kuma in zai gwada abu, kamar ya'di ko abinda yake da tsawo to yayishi dai dai
8→ Idan mutum zaiyi magana akan kowanene to yayi adalchi, koda kuwa makusancinsa ne, kamar uba, ko xa, ko 'yan uwa, haka nan kuma komai qiyayyarsa da wani, shima yayi masa adalci
9→ Haka kuma mutum idan ya xauki alqawari to ya cika, musamman alqawarin Allaah, san nan kuma alqawarin da yayi da mutane, ko hukuma, ko kuma wa'yanda ba musulmi ba
10→ Mutum yabi hanyar manzo (s.a.w) ,kada ya kuskura yabi wasu hanyoyi na shaixan, domin xai rabashi dda hanyar manzo (s.a.w), dukkan abinda babu hatimin Annabi (s.a.w) akai, to kada mutum yayi, komai kuwa yawan jama'ar da sukeyi
To wa'yan nan sune Allaah yake kira ga masu hankali da tunani da kuma tsoron Allaah suyi ko su bari,
kuma sune tsira ga duk wanda yayi aiki da wasiyyar
*Uba a wajen ahlul baiti*