KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) A NAN
Tarihin ANNABI (s.a.w)
Manzo Muhammad Al-Habib ɗan Abdullahi (Sallallahu alaihi wa sallam)
Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muammad ibn Abd Allāh ibn Abd al-Mudalib ibn Hāshim ibn Abd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha) Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.
Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in
Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi
Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma waxanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a voye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa
Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi xauki ba daxi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini
Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi xan Akhdabl
'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faxima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum
Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMuxallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Xalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas
Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali xan Abi Xalib (a.s) da Hasan xan Ali da Husain xan Ali da Aliyyu xan Husaini da Muhammad xan Ali da Ja'afar xan Muhammad da Musa xan Ja'afar da Ali xan Musa da Muhammad xan Ali da Ali xan Muhammad da Alhasan xan Ali da Muhammad xan Hasan Mahadi (a.s)
Mai tsaron qofarsa: Anas xan Malik. Mawaqinsa: Hassan xan Sabit, da Abdullahi xan Rawahata, da Ka'abu xan Malik
Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi xan Ummu Maktum da Sa'ad Al-kirdi
Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63
Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23
Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H
Wajan da ya yi wafati: Madina
Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Maxaukaki Mai alfarma
Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne qarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaxai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa qarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaxai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki xaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W)
Shi ne Muhammad xan Abdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan vollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa)